at-Tin (التِّين)

Abubakar Mahmoud Gumi by Abubakar Mahmoud Gumi

Chapter 95 • 8 verses • Meccan

95:1 Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.
95:2 Da Dũr Sĩnĩna.
95:3 Da wannan gari amintacce.
95:4 Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.
95:5 Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni
95:6 Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.
95:7 To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?
95:8 Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?